Zanga-zanga ta kazanta
Jami'an tsaron Sudan na kokarin tabbatar da ikonsu a babban birnin kasar Khartoum, bayan hallaka sama da farar hula 30 wadanda ba sa dauke da wani makami, a yayin tarwatsa masu zanga-zangar tabbatar da dumokuradiyya.
Ana iya ganin dakarun wata kungiyar mayakan sa-kai ta gwamnati wadanda ake jin tsoronsu, suna ta sintiri a birnin, inda rahotanni ke cewa suna harbi da duka da kuma kama fararen hula.
Ana ganin kusan 'yan kawanaki kadan kawai da suka gabata 'yan hamayyar na Sudan ke dab da cimma yarjejeniya da sojojin da ke rikon-kwarya na kasar, kan kafa gwamnatin farar-hula, sai kwatsam al'amura suka tabarbare.
Dakaru masu alaka da gwamnati da ke tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshan, sun yi nasarar korar wasu fararen hular, lamarin da ya kai ga sun bar dandalin da suka mamaye, suka ja baya zuwa cikin unguwanni inda gidajen jama'a suke.
Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ci gaba da kakkafa shingaye na datse hanyoyi da duwatsu da kuma tayoyi da suke cinna wa wuta.
Su kuwa dakarun mayakan sa-kai na gwanmnati suna ta sintiri na titunan a birnin a motoci inda suke kokarin kawar da shingayen, suna harbi da dukan masu zanga-zangar da kulake ko sanduna kamar yadda rahotanni suka ce.
Akwai rahotannin da ke nuna cewa an samu karin yawan mutanen da aka hallaka, kuma masu lura da yadda lamarin ke tafiya na ganin rikicin zai iya kazanta.
Wata mata da BBC ta yi hira da ita ta ce tana jin tsoron fita daga gida a yanzu saboda yadda jami'an tsaron na gwamnati ke harbi da dukan jama'a.
No comments
Post a Comment