An daure Yariman Saudiyya na jabu kan damfara
Yariman na jabu mai suna Anthony Gignac ya gamu da gamonsa ne bayan da 'yan sanda suka kama shi suka kuma mika shi gaban kuliya.
A tsawon shekaru kusan 30, Anthony Gignac ya ayyana kansa a matsayin Yariman Saudiyya don ya cuci mutane a fadin duniya, inji babbar mai sharia ta Amurka, Fajardo Orshan.
Wani alkali a jihar Florida ya bayyana Gignac mai shekara 48 da haihuwa a matsayin dan danfara da ya yi rayuwa a matsayin dan masarautar Saudiyya.
Mai shari'ar ta yanke wa Yariman na boge daurin shekara 18 a gidan kaso bisa laifin zamba cikin aminci.
- 'Yadda bashi ya yi wa wasu jihohin Najeriya katutu'
- Yadda dinkin sallar bana ya kasance a Kano
- Ko kun san alfanun bayar da zakkar fidda kai?
A cewar bayanan kotun, an kama Gignac sau 11 a cikin shekaru 30 da suka wuce sakamakon "danfara da sunan Yarima."
Daga farkon watan Mayu na shekarar 2015, ya yi amfani da sunan Khalid Bin Al-Saud, inji ofishin babban alkalin Amurka na yankin Kudancin Florida.
Anthony mai shekera 30 ya rinka saka gwala-gwalai masu tsada sannan yana bulaguro cikin jiragen sama da motoci na alfarma masu dauke da lambobin diflomasiyya.
Yariman na karya ya kuma rika amfani da katin da ke nuna shi a matsayin wani Sarki.
Bincike ya gano cewa ya yi damfara ta dalar Amurka miliyan 8.
Mista Gignac ya kasance yana saka tufafin saudiyya na gargajiya yana kuma sa agogon hannu da zobuna masu tsadar gaske.
Yana yawan tafiye-tafiyensa kan jiragen sama masu zaman kansu kuma yana tattara kayan al'adu masu tsada.
No comments
Post a Comment