Breaking News

Gwamna Ganduje ya yi sallar Idi a bayan Sarki Sanusi

Tun wani taron addu'a da Sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu ya shirya bayan cin zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje karo na biyu, inda kuma Gwamna Gandujen ya halarta, ba a sake ganin mutanen biyu ba wuri guda sai a ranar Talatar nan.
Gwamna Abdullahi ya Ganduje ya halarci sallar Idi da Sarki Sanusi ya jagoranta a filin Idi na Kofar Mata da ke birnin na Kano.
Da farko dai bayanai sun baza gari cewa Gwamna Ganduje zai yi sallar idin ne a garin Bichi, daya daga cikin sabbin masarautun da gwamnan ya yi a baya-bayan nan.
Kwatsam ba bu tsammani sai Gwamna Ganduje ya bayyana a filin masallacin da Sarki Sanusi ne yake jagorantar sallar.
Bisa al'ada Sarki da Gwamna kan gaisa kafin tayar da sallah da kuma bayan idar da huduba. Hakan ne kuma ya faru tsakanin shugabannin biyu.

'Yar hatsaniya ta kaure

Wakilinmu na Kano, Khalipha Dokaji ya tabbatar mana cewa an samu wata 'yar hatsaniya lokacin da aka idar da sallar idi tsakanin magoya bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da na gwamna Ganduje.
An ce magoya bayan Abba Kabir Yusuf na ta faman yi wa Sarki Sanusi kirari cewa "Kano ta Sarki daya ce" sannan wasu na cewa "Kano ta Sarki Sanusi ce".
Wadannan kalamai ne suka harzuka magoya bayan Gwamna Ganduje inda su ma suka fara yi wa nasu gwanin taken "Kano ta Uban Abba ce", al'amarin da ya janyo kaurewar hatsaniya.
Wakilin namu ya tabbatar wa da BBC cewa dukkanin bangarorin biyu sun zaro makamai kuma har an dan kwafsa al'amarin da ya janyo sauran masallata tserewa.
Babu dai wani rahoto kan cewa an samu wadanda suka jikkata sanadiyyar hatsaniyar.
Sai dai an fasa rumfar gilas din da Sarki Sanusi yake shiga ciki ya ja sallah sakamakon artabun.

Me Sarki Sanusi Ya fada?

Ganduje da Sarki Sanusi sun sanya zare
Image captionSarki Sanusi yana huduba a gaban Gwamna Ganduje da mataimakinsa
Bayan kammala huduba, mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira ga 'yan siyasa da su guji tayar da hasuma musamman a dai-dai lokacin da ba a dade da kammala azumin watan Ramadan ba.
Ya kuma bukace su da su rinka jan kunnen magoya baya kasancewar duk abin da za su aikata alhakin na rataye a wuyansu ne.
An dai ce kalaman na Sarki ba sa cikin hudubar da Sarkin ya tsara zai yi kasancewar ko dai ba a tsammacin hatsaniyar ba ko kuma Sarkin bai san Gwamna zai je masallacin idin na Kofar Mata ba.
Sai dai wasu na ganin Sarkin ya samu damar bayyana abin da yake ci masa tuwo a kwarya ne.

Ganduje bai je Gidan Shettima ba

Bisa al'ada, bayan kammala sallar Idi, Sarki na komawa gidan domin yin hawan sallah inda hakimai kan kai gaisuwa da caffa.
Shi ma gwamna ya kan dan koma gida ya sha ruwa sai ya fito zuwa gidan Sarki inda ake hawan sallar.
To amma a wannan karon ba a ga Gwamna Ganduje ba duk kuwa da cewa ya je masallaci ya yi salla a bayan sarki Sanusi.
Wasu dai na alakanta hakan da tsoron abin da ka iya faruwa da Gwamnan kamar ihu, idan ya halarci wurin mai cike da dimbin jama'a.
Akwai kuma masu ganin hakan ba ya rasa nasaba da kulalliyar da take tsakanin shugabannin biyu.

Hakiman da suka baro sabbin masarautunsu zuwa Kano

Masu sarauta
Image captionWasu daga cikin Hakiman Sarki da suka halarci sallar Idi a babban filin Idi na Kofar Mata
Wasu hakiman da ke karkashin sabbin masarautun da Gwamna Ganduje ya kirkira guda hudu sun bar masarautun nasu zuwa birnin Kano domin yin sallar idi da hawan sallah.
  • Dan Isan Kano hakimin Warawa
  • Dokajin Kano hakimin Garko
  • Dan Galadiman Kano hakimin Bebeji
  • Sarkin Shanun Kano, hakimin Rimin Gado
  • Yariman Kano hakimin Takai
  • Barden Kano hakimin Bichi
  • Sarkin Fulanin Ja'idanawa Hakimin Garun Mallan
  • Makaman Kano hakimin Wudil
  • Sarkin Dawaki mai Tuta hakimin Gabasawa
  • Dan Kadai Kano hakimin Tudun Wada
  • Dan Madami hakimin Kiru
  • Dan Amar Din Kano Hakimin Doguwa
  • Madakin Kano hakimin Dawakin Tofa
Da dama wadanda aka fitar da su daga Knao sun je Knaon sallah
Image captionGwamna Ganduje da mataimakinsa a cikin masu sarauta
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko Gwamnan Ganduje zai halarci hawan durbar da ake yi washegarin sallah a kofar gidan Sarkin.
Sannan ko shi ma Sarki Sanusi zai ziyarci gwamnan a hawan Nasarawa da ake yi kwanaki biyu bayan sallah.
A baya dai Sarki Sanusi bai halarci bikin rantsar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba da aka yi ranar 29 ga watan Mayu.
Sai dai dukkanin sabbin sarakan wato na Bichi da Karaye da Gaya da Rano sun halarci bikin.
Sarki Sanusi ya halarci rantsar da gwamna Ganduje a wa'adin farko a shekarar 2015.
Sarakai uku ne suka halarci bikin rantsar da Ganduje
Image captionSarkin Bichi Aminu Ado Bayero ya halarci rantsar da Ganduje
A 'yan makonnin da suka gabata ne dai masarautar ta Kano ta ce har yanzu mai marataba sarki Sanusi II ne abin biyayya ga hakimai da dagatan kananan hukumomi 44 na jihar.
Wata sanarwa daga masarautar Kanon mai dauke da sa hannun Awaisu Abbas Sanusi ta bukaci masu rike da sarautun gargajiya da su ci gaba da karbar umarni daga sarki Sanusi.
Sanarwar ta ce ta bayar da umarnin ne kasancewar batun na gaban kotu.
Har wa yau, masarautar ta shaida wa hakiman da dagatan cewa ka da su ji tsoron yi mata biyayya domin ta tanadi jerin lauyoyin da za su kare su ko da za a ci mutuncinsu.
Sanarwar ta kara da neman masu rike da sarautun gargajiyar da su tsananta addu'o'in ganin yanayin da masarautar take ciki bai dore ba.
Gwamna Abdullahi Umar GandujeHakkin mallakar hotoSALIHU TANKO YAKASAI/FACEBOOK
Image captionGwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce bai sami umarnin Kotu kan dakatar da nadin sabbin sarakuna a Kano ba.
Masana harkokin shari'a a Najeriya dai na ci gaba da tofa albarkacinsu dangane da wannan batu mai sarkakiya tsakanin masarautar ta Kano da bangaren gwamnati.
Ko a baya ma lauyoyin sun ce bangaren gwamnati ya bijire wa umarnin wata babbar kotu bayan nadin sababbin sarakuna hudu a jihar.
Wata lauya mai zaman kanta a jihar, Barrista Maryam Abubakar ta ce la'akari da abubuwan da suka faru a baya, bijirewa umarnin kotu ba wani sabon abu ba ne.
Ta ce a baya an sha bayar da irin wannan umarni har a gwamnatin tarayya amma sai ka ga an bijire, sai dai hanzarin da gwamnati ta bayar shi ne ita ba ta karbi kowane umarni daga kotun ba.
Amma lauyar ta ce duk da cewa gwamnati ta bayar da nata uzurin da ta fake a kai, wadanda suka shigar da karar na da damar su sake shigar da cewa lallai an karya umarnin kotu.
Kalaman lauyar na zuwa ne bayan gwamnatin Kanon ta mika wa sabbin sarakunan masarautu hudu da ta kirkira sandunan girma.
Gwamnatin dai ta yi gaban kanta duk kuwa da umurnin da wata babbar kotu ta bayar cewar ta dakatar da duk wata harkar da ta shafi kafa masarautun zuwa lokacin da za ta saurari karar da ke gabanta.
Sai dai gwamnatin jihar Kanon ba ta bi umarnin ba, don ba ta karbi wani sako mai kamar hakan ba, sai dai kawai ta ga ana yada wa a shafukan sada zumunta.
Tun a ranar Lahadi gwamna Ganduje ya mika wa sarakunan sanda, amma a wata masarautar sai cikin dare aka yi bikin.
Gwamnatin Kano ta ce a shafukan sada zumunta kawai ta ji batun da ake yadawa game da umarnin babbar kotu, wanda kuma a cewarta bai isa hujja ba.
kanoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionSarki Sanusi
Sai dai Barista Maryam ta ce idan har kotu ta bayar da irin wannan umarni wanda ba lallai ya kasance hannu da hannu ba - yana iya zama ta hannun wani ko ta jaridu da ma kafafan sada zumunta - ya zama wajibi a mutunta umarninta.
''In dai kotu ta bayar da umarni har aka wallafata to ya zama dole doka ta yi aikinta, kuma a bi umarninta ba lallai wai sai hannu da hannu ba.''
Lauyar ta kuma ce duk wanda aka samu da yin gaban kansa to laifi ne mai zaman kansa, kuma ana iya kai mutum kotu a hukunta shi a kan hakan.
Yadda aka raba masarautun Kano
Image captionYadda aka raba masarautun Kano
Masana shari'a dai na ganin cewa an yi gaggawa wajen aiwatar da wannan doka, ganin yadda komai cikin sa'o'i 72 aka aiwatar.
''A sani na wannan shi ne karon farko da kudirin doka ya tsallake karatun farko da na biyu da uku har aka sa mata hannu a cikin kankanin lokaci,'' in ji Barrista Maryam
Har yanzu dai takaddama ba ta kare ba kan wannan nadin, inda wasu ke ganin a matsayin bi-ta-da-kulli saboda takun-sakar da ake zargin ya wanzu tsakanin sarki Muhammadu Sunusi na II da gwamnati, batun da Gwamna Ganduje ya musanta.

No comments