Facebook ya rufe kamfanin Isra'ila da ya yi katsalandan a zaben Najeriya
Facebook ya dakatar da wani kamfanin Isra'ila da ya yi amannar yana da hannu wajen bude wasu daruruwan shafukan boge da zauruka da kuma yin katsalandan a zabukan Najeriya da wasu kasashen Afirka shida.
Kamfanin ya ce wadanda suka aikata abin da Facebook din ya kira "aikin rashin da'a" sun yi kutse a Najeriya da Senegal da Togo da Angola da Nijar da kuma Tunisiya.
Sun yi ta wallafa labarai da sharhi a kan babban zaben Najeriya kuma sun kunshi ra'ayoyi daga 'yan takara da kuma yadda suke sukar abokan hamayyarsu.
Suna da sunaye kamar Hidden Africa da kuma Secret Democratic of Congo.
Wani bayani da suka wallafa ya yi kama da goyon bayan shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi, kuma suka nemi dan takarar jam'iyyar hamayya da ya karbi shan-kaye.
Facebook ya ce wadannan kamfanoni sun fara harkokinsu ne a kasar Isra'ila kuma suna harkoki a yankin Latin Amurka da kuma kudancin nahiyar Asiya.
Shugaban sashen kula da tsaron shafin Facebook Nathaniel Gleicher ya ce sun rufe shafuka da zauruka da kuma bayanai har 265 a Facebook da Instagram da suka ce sun saba ka'idojin kamfanin.
Wadanda suka aikata abin sun kashe kudi kusan dala 812,000 tsakanin Disambar 2012 zuwa Afrilun 2019.
Kasashe biyar daga cikin shidan sun gudanar da zabukansu tun 2016, inda Tunisiya za ta gudanar da nata nan gaba a wannan shekara.
An zargi wani kamfani mai suna Cambridge Analytica, wanda yanzu babu shi da yin kutse ga zabuka a kasashen Afirka kamar Najeriya da Kenya ta kafar Facebook.
Mahukuntan Facebook sun shaida wa BBC cewa sun lura da irin dabarun da ake amfani da su wajen yin katsalandan ga kasashen Afirka.
Yayin zaben kasar Afirka Ta Kudu, Facebook ya rika yin talla a manyan jaridun kasar don yaki da yada labaran karya a Whatsapp da sauran shafukan sada zumunta.
No comments
Post a Comment